Taskar Labarai

Sai an biya kudin fansa za mu saki mata 53 da muka sace a Katsina – ‘Yan bindiga

Sai an biya kudin fansa za mu saki mata 53 da muka sace a Katsina – ‘Yan bindiga

Sai an biya kudin fansa za mu saki mata 53 da muka sace a Katsina – 'Yan bindiga
Sai an biya kudin fansa za mu saki mata 53 da muka sace a Katsina – ‘Yan bindiga

Yan bindigar da suka sace mata 53 da ke rakiyar kai wata amarya a jihar Katsina a makon da ya gabata, sun saki wani bidiyo da ke nuna matan tsaye cikin daji.

A ranar Alhamis da daddare ne ‘yan bindigar suka yi garkuwa da matan masu rakiyar amarya har da direban motar da suke ciki a karamar hukumar Sabuwa da ke jihar ta Katsina.

A bidiyon mai tsawon minti 2:20, an ga dan bindiga sanye da kayan sojoji dauke da bindiga. Sun nuna matan sanye da hijabi a tsaye cikin surkukin daji. Cikin matan, akwai guda biyu masu rike da jariri.

Bidiyon ya nuna amaryar sanye da kakin soji da bindiga a wuyanta sai wani mutum wanda bisa jawaban ‘yan bindigar ke nuna shi ne direban motar da wata mata dukkansu rataye da bindiga a wuya.

Domin Samun Ingatattun Labaran Hausa ku cigaba da bibiyar wannan shafi namu mai Albarka

Related Articles

Back to top button