Taskar Labarai

CBN ya musanta musanya kuɗaɗen waje da mutane suka ajiye a bankuna zuwa naira

CBN ya musanta musanya kuɗaɗen waje da mutane suka ajiye a bankuna zuwa naira

Babban Bankin Najeriya CBN ya musanta wasu rahotonni da ke cewa yana shirin musanya kuɗaɗen waje da mutane suka ajiye a bankuna zuwa naira.

Wasu kafofin yaɗa labarai a ƙasar ne suka yi zargin cewa gwamnatin ƙasar na shirin musanya kuɗaɗen waje da mutane ke ajiyewa a bankunan ƙasar zuwa naira.

To amma cikin wata sanarwa CBN ɗin ya fitar, ya ce labarin ba shi da ƙanshin gaskiya, kuma an yaɗa shi da nufin haifar da ruɗani a kasuwar musayar kuɗaɗen waje ta ƙasar, wadda babban bankin ya ce yake ƙoƙarin ganin ta daidaita.

Sanarwar ta ƙara da cewa a ‘yan watannin da suka gabat ma a an yaɗa irin wadannan ƙarairayi, kuma bankin ya ce ana yin hakan ne da nufin yin zagon-ƙasa ga ƙoƙarin da yake yi.

“Muna tabbatar wa da al’umma cewa, CBN na bakin ƙoƙarinsa don samar wa mutane ƙwarin gwiwwa, kuma bankin ba zai taɓa yin abin da zai rage darajar kuɗaɗe da tattalin arzikin mutane ba”, in ji sanarwar.

CBN ɗin ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki, da su yi watsi da waɗancan labaran da ya ce na ”ƙoƙarin kawo ruɗani ga tsarin ajiyar kuɗaɗen waje”, wanda CBN ya ce ana ƙirƙirarsu ne don yin zagon-ƙasa ga tsare-tsarensa.

Babban Bankin ya kuma gargaɗi masu ƙirƙirar irin waɗannan labaran da cewa hakan ka iya haifar da durƙushewar tattalin arzikin ƙasar.

Related Articles

Back to top button