Taskar Labarai

Ankai Harin Jirgin Kasa a Faransa

Ankai Harin Jirgin Kasa a Faransa

Anakai Harin Jirgin Kasa a Faransa
Ankai Harin Jirgin Kasa a Faransa

Aƙalla mutum uku sun jikkata sakamakon wani harin wuƙa da aka kai tashar jirgin ƙasa a birnin Paris na ƙasar Faransa.

Jami’ai sun ce mutum guda ya samu munanan raunuka bayan da aka daɓa masa wuƙa a ciki a harin da ya auku a unguwar Gare Lyon.

‘Yan sandan Faransa sun ce sun kama wani mutum da suke zargi da hannu a harin.

Rahotonni sun ce asalin mutumin ɗan kasar Mali ne, to amma ya gabatar wa ‘yan sanda takardun Italiya.

Ba a dai danganta harin nasa da na ta’addanci ba.

Tuni dai aka dakatar da jigilar jiragen ƙasa tsakanin tsakiya da kudancin birnin Paris zuwa ƙasashen Italiya da Switzerland.

Related Articles

Back to top button